5 Yuni 2015 - 10:09

Ruhotannin sun tabbatar da cewa mutane 31 aka tabbatar da mutuwarsu bayan da wani dan kunar bakin wake ya tayar da bom a wata babbar kasuwa da ke Jimeta a Jihar Adamawa arewacin Najeriya.Babban Jami’in Kungiyar Agajin gaggawa ta NEMA Sa’ad Bello ya ce sun samu gawarwakin mutane 31 da kuma 38 da ke kwance a gadon Asibiti.

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Adamawa tace bayan idar da Sallar Magariba a jiya Alhamis dan kunar bakin wake ya tayar da bom a kasuwar Fallujah a Jimeta.

Wannan na zuwa ne bayan an kai wani harin Bom a garin Maiduguri a jiya Alhamis inda wata budaddiyar mota da abkawa wani shingen bincike a kusa da barikin Sojoji.

Jerin hare haren na zuwa a yayin da sabon Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ke kammala ziyara a kasashen Nijar da Chadi kan yadda za a kawo karshen mayakan Boko Haram da ke addabar yankin arewa maso gabaci da kuma kasashen da ke kewaye da tabkin Chadi.ABNA